Jiragen Yakin Masar Sun Kashe 'yan Ta'adda A yankin Sinaa
Jiragen Yakin Masar Sun Kai hari a yankuna daban-daban na yankin Sinaa
Kamfanin Dillancin Labarun Anatoli daga birnin alqahira, ya ambato cewa; A jiya asabar jiragen yakin kasar ta Masar sun kai hare-hare a garin Rafah da ke kan iyala da Palasdinu.
Rahoton ya ci gaba da cewa 'yan ta'adda 27 ne su ka halaka daga cikinsu hadda daya daga cikin kwamandojin kungiyar mai alaka da Da'esh.
Majiyar tsaron Masar ta ce; Tankar yakin Masar ta yi nasarar kashe daya daga cikin kwararru maharban kungiyar 'yan ta'addar.
Kwanaki 10 da su ka gabata sojojin Masar din sun sanar da kashe kwamandan kungiyar "Ansaru baitul muqaddas", da ake kira Abu Du'a al-Ansary , tare da wasu mutane 45 da su ke a tare da shi.
Tun bayan saukar da Muhammadu Mursi daga kan mulki a 2013 ayyukan ta'addanci su ka tsananta a kasar ta Masar.