MNSD Nasara za ta shiga cikin Gwamnati a Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9643-mnsd_nasara_za_ta_shiga_cikin_gwamnati_a_nijer
Jam'iyar Adawa ta MNSD Nasara a Nijer ta karba kira Shugaba Issoufou na shiga cikin Gwamnati
(last modified 2018-08-22T06:58:46+00:00 )
Aug 15, 2016 02:00 UTC
  • MNSD Nasara za ta shiga cikin Gwamnati a Nijer

Jam'iyar Adawa ta MNSD Nasara a Nijer ta karba kira Shugaba Issoufou na shiga cikin Gwamnati

Kamfanin dillancin Labaran Kasar Faransa ya nakalto Tidjanin Abdoul-kadri babban saktaren Jami'iyar na cewa Jam'iyyar ta MNSD Nassara karkashin jagorancin Alhaji Seini Oumarou da ke cikin kawancen jam'iyun adawa , ta amince za ta shiga gwamantin Shugaba Issoufou Mahamadou bayan kiran da shugaban kasar ya yi na kafa gwamnatin hadaka domin ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki na matsalar cin hanci da rashawa.

 Cikin jawabinsa na bikin tunawa da ranar da Jamhuriyar ta Nijar ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Faransa ya bukaci shigar yan adawa a cikin gwamnatinsa. Jam'iyyar ta MNSD ta bayyana wannan kudiri nata , bayan wani taron muhawara da wakilan jam'iyyar da suka fito daga jihohin kasar suka gudanar a Yamai babban birnin kasar, inda mambobin kwamitin kolin jama'iyyar 148 daga cikin 203 suka halarci taron, kana 144 suka amince da matakin.

A halin da ake ciki, jam'iyar MNSD Nasara nada kujeru 20 a Majalisar dokokin kasar kuma shugaban ta ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 21 ga watan Favrayun da ya gabata. Sai dai har yanzu babu wani martani dag bangaren adawa ko masu rinjaye kan wannan mataki na MNSD.

Tun bayan zaben shugaba Issoufou a matsayin shugaban kasa karo na biyu,Jumhoriyar ta Nijer ta shiga ciki wani yanayi, inda a halin da ake ciki kasar ta fuskantar matsalar biyan albashi musaman na maliman makaranta.