'Yan sanda sun buda wata ga masu zanga-zanga a Dimokaradiyar Kwango
(last modified Wed, 17 Aug 2016 18:14:54 GMT )
Aug 17, 2016 18:14 UTC
  • 'Yan sanda sun buda wata ga masu zanga-zanga a Dimokaradiyar Kwango

Majiyar Labaran kasar Kwango sun sanar da mutuwa tare da jikkatar wasu mahalarta zanga-zanga bayan da jami'an 'yan sanda suka bude musu wuta

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar labaran kasar Dimokaradiyar Kwango na cewa wani Mutum guda ya rasa ransa yayin da wasu biyar na daban suka  jikkata sanadiyar buda wuta  da jami'an 'yan sanda suka yi kan mahalarta zanga zanga a kokarin da suke na tarwatsa su a garin Beni da ke gabashin Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo inda aka kashe fararen hula 51 a makun da ya gabata.

Shugaban kungiyoyin fararen hula na Beni Gilbert Kambale ya ce matashin ya rasa ransa ne a kusa koramar Kilokwa, bayan da wani dan sanda ya bindige shi.

A farkon wannan maku  da muke ciki ne aka kara yawan jami’an tsaro a manyan hanyoyin garin na Beni bayan taron da masu zanga zangar suke saboda alhinin kashe fararen hula 51.

Dandazon mutane dake kona tutocin jam’iyya mai mulkin kasar sun zargi gwamnatin Janhuriyyar Congon karkashin shugaba Joseph Kabila da gazawa wajen tsare rayukan mutane a yankin.

Daga watan Oktoban shekara ta 2014 zuwa yanzu sama da mutane 650 aka kashe a ciki da wajen garin Beni, kashe kashen da gwamnatin kasar ke zargin kungiyar ‘yan tawayen ADF da aikatawa, wadda ke da tushe a kasar Uganda.