Tashin Bom A Yankin Sinaa Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9886-tashin_bom_a_yankin_sinaa_na_kasar_masar
Harin Ta'addanci A Yankin Sinaa
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 20, 2016 04:02 UTC
  • Tashin Bom A Yankin  Sinaa Na Kasar Masar

Harin Ta'addanci A Yankin Sinaa

Kamfanin Dillancin Labarun Sputnik ya ambato majiyar tsaron kasar Masar na cewa; An sami asarar rai da jikkata a sanadiyyar wani harin ta'addanci da aka kai a yankin Sinaa.

Harin na jiya juma'a an kai shi ne a garin al-arish da ke yankin na Sinaa, wanda ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda da kuma jikkata wasu sojoji biyar.

A ranar alhamis din da ta gabata ma dai sojojin kasar ta Masar biyu sun mutu bayan harbinsa da bindiga da aka yi a yankin na Sinaa.

Tun sauke Muhammad Mursi daga kan mukaminsa na shugabancin kasar a 2013 ne, 'yan ta'adda su ka bude yaki da gwamnatin Masar.