NIjar : Kotu Taki Bada Belin Masu Zargin Juyin Mulki
A Nijar, bangaren bincike na kotun soji a Yamai babban birnin kasar ya yi wasti da bukatar bada belin mutanen da ake zargi da hannu a kokarin yin juyin mulki wa gwamantin kasar a watan Disamba bara.
koda yake labarin bai kawo cikakun hujoji ba dangane da watsi da bukatar, aman daya daga cikin lauyoyin dake kare mutanen ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa suna nazari kan matakin kotun kafin yin bayani.
Idan ana tune, shugaban kasar ne Mahamadu Issufu ya sanar a kasar shekara 2015 data gabata cewa jami'an leken asiri na kasar sun murkushe wani yunkurin juyin mulki wa gwamnatinsa.
Bayan yunkurin juyin mulkin ne aka cafke mutane kimanin 20 da suka hada da fararen hula da mayan sojoji da dama ciki har da wani Janar.
Galibin fararen hula da ake tsare da 'yan adawa ne na jam'iyyar Moden Lumana.