Da'esh Ta Kashe Sojojin Masar
Feb 19, 2016 09:12 UTC
Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta dauki alhakin kashe sojojin Masar biyu.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya nakalto wata sanarwa da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ( Isil) ta yi na daukar alhakin kashe wasu mutane biyu da ta bayyana a matsayin 'yan leken asirin sojan Masar.
A jiya juma da marece ne dai kungiyar ta Da'esh ta fitar da hoton da ta sanya a sahfin Twitter inda ta ke fille kawukan mutanen biyu da ta kira 'yan leken asirin sojojin da su ka yi ridda" kamar yadda ta saba kiran sojan kasar Masar.
A baya ma dai 'yan ta'addar sun sha nuna yadda su ke kashe sojojin Masar da su ke zargi da yi musu leken asiri.
Tags