-
Najeriya: Dalibai 105 Suka Bata, Bayan Harin Boko Haram A Makarantar Dapchi
Feb 23, 2018 14:37Iyayen 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi dake arewa maso gabashin Najeriya, sun ce dalibai 105 ne basu amsa kira ba bayan harin da ake kyautata zaton mayakan Boko haram sun kai a makarantar a ranar Lahadi data gabata.
-
G5 Sahel Ta Samu Cike Gibin Kudaden Da Take Bukata A Brussels
Feb 23, 2018 14:12Kungiyar kasashen nan biyar na yankin Sahel, ta samu kudaden da take bukata a wani taro neman tallafi na kungiyar da ya gudana yau Juma'a a birnin Brussels na kasar Belgium.
-
Sudan Ta Kudu : An Yanke Wa Wani Tsohon Kanal Na Afrika Ta Kudu Hukuncin Kisa
Feb 23, 2018 12:07Wata kotu a Sudan ta Kudu ta yanke hukuncin kisa ga wani tsohon kanal na sojin Afrika ta Kudu, bisa tuhumarsa da yunkurin kifar da gwamnati.
-
ECOWAS Za Ta Aiwatar Da Shirin Kudi Na Bai Daya A Shekara Ta 2020
Feb 23, 2018 08:18Shuwagabannin Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) sun sha alwashin aiwatar da shirin kudi bai daya a tsakanin kasashen a shekara ta 2020 kamar yadda suka tsara
-
Cutar Amai Da Gudawa Ta Kashe Yan Gudun Hijira 26 Cikin 552 Da Suka Kamu Da Ita A Congo
Feb 23, 2018 08:17Yan Gudun Hijira 26 ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar amai da gudawa daga cikin mutane 552 da suka kamu da ita a kasar Demokradiyyar Congo .
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Tsananin Damuwarta Kan Matsalolin Kasar Afrika Ta Tsakiya
Feb 23, 2018 02:14Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hanzarta daukan matakan gaggawa da nufin shawo kan tarin matsalolin da suke addabar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
-
Jiragen Saman Yakin Amurka Sun Kai Hari Kan Sansanin Kungiyar Al-Shabab Na Somaliya
Feb 23, 2018 02:09Jaragen saman yakin kasar Amurka marassa matuka ciki sun kaddamar da hare-hare kan sansanin mayakan kungiyar Al-Shabab na Somaliya, inda suka kashe 'yan ta'adda akalla hudu.
-
Sojojin Masar sun kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da Saba'in A Yankin Sina Ta Arewa Na Kasar
Feb 23, 2018 02:07Kakakin rundunar sojin Masar ya sanar da cewa: Tun daga farkon wannan shekara ta 2018 zuwa yanzu; sojojin kasar sun kashe 'yan ta'adda da yawansu ya kai 71 a yankunan lardin Sina da ke arewacin kasar.
-
Ana Ci Gaba Da Samun Labarai Masu Karo Da Juna Kan Makomar 'Yan Matan Dapchi
Feb 22, 2018 14:12Ana ci gaba da samun labarai masu karo da juna dangane da makomar 'yan matan makarantar mata ta Dapchi da ke jihar Yobe da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai wa hari a ranar Litinin din da ta gabata, wasu kafafen watsa labarai sun ce an gano gawar wasu 'yan matan su biyu a daidai lokacin da gwamnan jihar Yobe din kuma yake kiran iyayen yaran da su ci gaba da addu'oin gano 'ya'yan nasu.
-
Gwamnatin Kamaru Ta Kafa Wani Sansanin Soji A Yankin Bamenda Don Tabbatar Da Tsaro
Feb 22, 2018 14:11Gwamnatin Kamarun ta sanar da kirkiro wani sabon yanki na soji don tabbatar da tsaron da ake bukata yankin Yamma da Arewa maso yamma na kasar a kokarin da gwamnatin ta ke yi na fada da 'yan awaren yankunan kasar masu magana da harshen Turanci.