Najeriya: Dalibai 105 Suka Bata, Bayan Harin Boko Haram A Makarantar Dapchi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28501-najeriya_dalibai_105_suka_bata_bayan_harin_boko_haram_a_makarantar_dapchi
Iyayen 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi dake arewa maso gabashin Najeriya, sun ce dalibai 105 ne basu amsa kira ba bayan harin da ake kyautata zaton mayakan Boko haram sun kai a makarantar a ranar Lahadi data gabata.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 23, 2018 14:37 UTC
  • Najeriya: Dalibai 105 Suka Bata, Bayan Harin Boko Haram A Makarantar Dapchi

Iyayen 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi dake arewa maso gabashin Najeriya, sun ce dalibai 105 ne basu amsa kira ba bayan harin da ake kyautata zaton mayakan Boko haram sun kai a makarantar a ranar Lahadi data gabata.

Shugaban sabuwar kungiyar iyayen 'yan makarantar, Bashir Manzo, ya ce sun fitar da jerin sunayen 'yan makarantar, kuma 105 basu amsa kira ba, bayan cewa tun da farko aka hukumomi sun yaudare su ta hanyar sanar da cewa an ceto duk 'yan makarantar bayan harin.

Kwanaki kadan da kaddamar da harin, har yanzu hukumomin yankin sun katsa samun daidaito akan yawan 'yan makarantar da suka bata.

Wannan harin dai ya sake maimaita abunda ya faru kan 'yan makarantar sakandare ta Chibok 276, a watan Afrilu na 2014 da kungiyar Boko haram ta sace, a yayin da lamarin ke kara aza ayar tambaya ga 'yan kasar akan aikin tabbatar da tsaro na sojoji a shiyyar arewa maso gabashin kasar, duba da ikirarin da hukumomin kasar ke yi na cewa sun karya laggon kungiyar.