Rauhani: Amurka Ce Tushen Ta'addanci A Yankin Gabas Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10222-rauhani_amurka_ce_tushen_ta'addanci_a_yankin_gabas_ta_tsakiya
Shugaban Kasar Iran ya ce; Amurka ce tushen Ayyukan Ta'addanci A Kasashen wannan yankin.
(last modified 2018-11-18T05:33:40+00:00 )
Aug 27, 2016 14:26 UTC
  • Rauhani: Amurka Ce Tushen Ta'addanci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shugaban Kasar Iran ya ce; Amurka ce tushen Ayyukan Ta'addanci A Kasashen wannan yankin.

Shugaban na jamhuriyar musulunci ta Iran Sheikh Hassan Rauhani, wanda ya gabatar da jawabi a yau asabar ya ce; Idan ace Amurka ba ta kai wa Afghanistan da Afghanistan hari ba, kuma ba ta kirkiri rikici a kasar Syria ba, to da ta'addanci bai watsu kamar yadda ya ke a yanzu ba.

Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa;  Wajibi ne kasashen duniya su hada karfi da karfe domin fada da ayyukan ta'addancin kungiya irin Da'esh.

Shugaba Hassan Rauhani, ya ci gaba da cewa; Yaki, yana a matsayin barna ce, amma kare kai daukaka ce ga kasa, don haka wajibi ne ga kowace kasa ta yi gwagwarmaya domin korar masu wuce gona da iri.