Mahangar Jagora Dangane Da Fada Da Abokan Gaba.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10285-mahangar_jagora_dangane_da_fada_da_abokan_gaba.
Jagora:W ajibi ne ga makiya su fahimci cewa matukar su ka kawo wa Iran hari, to za su fuskanci maida  martani mai tsanani.
(last modified 2018-08-22T06:58:50+00:00 )
Aug 28, 2016 23:50 UTC
  • Mahangar Jagora Dangane Da Fada Da Abokan Gaba.

Jagora:W ajibi ne ga makiya su fahimci cewa matukar su ka kawo wa Iran hari, to za su fuskanci maida  martani mai tsanani.

A yayin ganawarsa da kwamandojin sojan saman jamhuriyar musulunci ta Iran, na rundunar Khatamul-Anbiya, ( s.aw.a.), jagoran juyin musulunci Ayatullah Uzma Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamnei, ya ce wajibi ne ga makiya su fahimci cewa matukar su ka kawo wa Iran hari, to za su fuskanci maida  martani mai tsanani.  Jagoran, ya shaidawa kwamandojin na sojan sama  a jiya lahadi cewa; Abokan gabar jamhuriyar musulunci ta Iran, mutane ne mayaudara masu fada da 'yancin al'umma.

Wani sashen na jawabin jagora y ace; Dole ne a kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar abokan gabar da su ke son raunana al'umma, ta yadda ba ma za su iya yin tunanin kawo hari ba.

Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran ta fuskanci barazana daga makiya. Domin juyin musulunci da nasararsa yana nufin yin watsi da kore ikon da tasirin da  manyan kasashe masu takama da karfi su ke da shi a cikin Iran.

Kiyayyar da kasashe masu takama da karfi bisa jagorancin Amurka su ke yi wa Iran, ba irin kiyayyar da aka saba da ita ba ce a tarihin yake-yake da zubar da jini da fifiko na siyasa. Kiyayya  ce ta tunani. Kiyayyar da tsari mai takama da karfi da kuma 'yan sahayoniya su ke yi wa Iran, yana da alaka ne da akida ta addini da cin gashin kai na al'ummar Iran. Su ne abubuwan da makiyan ba ashirye su ke su amince da su ba.Kiyayya ce wacce ta dauki salon jayayya a tsakanin gaskiya da karya.

A tsawon shekaru 37 na juyin musulunci, makiya sun yi duk abinda za su iya na nuna gaba. Sun yaki juyi na tsawon shekaru 8 ta hanyar tsarin ba'asiyya na Iraki. Sun kuma kakabawa Iran din takunkumin hana ta sayen duk wasu makamai na kare kanta. Manufarsu ita ce raunana Iran din da rusa cin gashin kan da ta ke da shi da kuma 'yancinta.

Wannan shi ne babbar alakar kiyayyar da su ke nuna wa jamhuriyar musulunci ta Iran, tun bayan cin nasarar juyinta.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma bayyana cewa; Abinda makiya su ke so, shi ne a zauna cikin rashin kariya, ta yadda a duk lokacin da su ka ga dama za su kawo hari.

Rundunar Khatamul-Anbiyah wacce ta ke kula da bada kariya ta sama ga Iran, tana daga cikin muhimman cibiyoyin tsaro da ake da su a Iran. Jagoran ya jaddada wa rundunar cewa wajibi ne ta kasance cikin shiri da kuma kara karfin da ta ke da shi domin yanke kaunar abokan gaba.