Shamkhani: Girman Kai Irin Na Jahiliyya Ne A Kwakwalen Masu Mulkin Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10864-shamkhani_girman_kai_irin_na_jahiliyya_ne_a_kwakwalen_masu_mulkin_saudiyya
Abinda Ya Faru a shekarar bara a Mina na mutuwar alhazai, ganganci ne da rashin tsari.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 10, 2016 14:30 UTC
  • Shamkhani: Girman Kai Irin Na Jahiliyya Ne A Kwakwalen Masu Mulkin Saudiyya

Abinda Ya Faru a shekarar bara a Mina na mutuwar alhazai, ganganci ne da rashin tsari.

Babban Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran ya ce; Abinda Ya Faru a shekarar bara a Mina na mutuwar alhazai, ganganci ne da rashin tsari.

Ali Shamkhani ya fada a yau asabar cewa; Iyalan Sa'ud da gwamnatinsu sun yi watsi da ka'ida ta farko ta hakkokin dan'adam, wanda shi ne kwantar da wadanda su ka jikkata a mima hankali. Haka nan kuma sun ki neman uzuri daga iyalan wadanda su ka yi shahada balle kuma su hukunta wadanda su ke da hannu a abinda ya faru.

Babban sakataren majalisar kolin ta tsaron kasar Iran, ya kuma yi ishara da yakar kasar Yamen da Saudiyyar ta ke yi tare da taimakon da haramtacciyar kasar Isra'ila,manufarsa ita ce fada da ma'abota 'yanci 'yan kasar Yamen.