Ziyarar Shugaban kasar Iran zuwa kasar Vietnam
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i11986-ziyarar_shugaban_kasar_iran_zuwa_kasar_vietnam
A wannan Laraba ce, Shugaban jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani zai kai ziyarar kwanaki biyu birnin Hanoi babban birnin kasar Vietnam
(last modified 2018-08-22T06:59:02+00:00 )
Oct 05, 2016 02:16 UTC
  • Ziyarar Shugaban kasar Iran zuwa kasar Vietnam

A wannan Laraba ce, Shugaban jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani zai kai ziyarar kwanaki biyu birnin Hanoi babban birnin kasar Vietnam

Shugaba Hasan Rauhani tare da takwaransa na kasar Viet Nam Trần Đại Quang a wani zama da za su yi tare da halartar shugabanin kasashen biyu a birnin Hanoi za su tattauna kan batun karfafa alaka a bangarori daban daban dake tsakanin kasashen biyu sannan kuma kasashen biyu za su sanya hanu kan wasu sabin kudirori tsakanin kasashen biyu.

A yayin wannan ziyara ta Shugaban Rauhani, wasu wakilan Majalisar Musulinci ta Iran dake cikin tawagar Shugaban kasar za su tattauna tare da takwarorin su na kasar Viet Nam musaman ma kan batun da ya shafi bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

A wannan Talatar Shugaba Rauhani ya gana da Salah Adibi Jadakar Jumhoriyar musulnci ta iran a kasar Viet Nam dangane da shirye-shiryen wannan ziyara, a karshen tattaunawar, a karshen tattaunawar,Mista Adib ya bayyana kyakkyawan fatan sa kan wannan ziyara ta kasance sanadiyar karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.shakka babu kasashen biyu suna wasu manufofi iri guda kamar fada da masu milkin mallaka, fada da zalinci da saurensu , da hakan ya sanya Al'ummar kasar Viet Nam ke da matsayi na musaman a idanun mutanan kasar Iran kuma wannan matsaya za ta taimaka wajen fadada alaka a tsakanin kasashen biyu.

Idan kuma aka yi la'akari da matsayin kasashen a yankin Asiya, inda kasar Iran ke taka muhimiyar rawa a yammacin Asiya, ita kuma kasar Vet Nam ke taka muhimiyar rawa musaman kan abin da ya shafi tattalin Arziki a kudu maso gabashin Asiya,