Juyayin Daren Tasu'a A Fadin Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i12262-juyayin_daren_tasu'a_a_fadin_iran
An Juyayin Daren Tasu'a A Fadin Iran
(last modified 2018-08-22T06:59:04+00:00 )
Oct 10, 2016 15:24 UTC
  • Juyayin Daren Tasu'a A Fadin Iran

An Juyayin Daren Tasu'a A Fadin Iran

Miliyoyin mutanen Iran suna ci gaba da yin juyayin shahidan karbala a wannan daren na Asu'a.

Cibiyoyin addini da suka hada da masallatai da Husainiyya a cikin birane da kauyuka ne wuraren da ake yin tarukan. Hubbaren Imam Ridha (a.s) da kuma na Fatima Ma'asumah da ke birnin Qum, suna daga cikin muhimman wuraren da dubun dubatar mutane su ka yi cincirindo domin juyayin shahadar Imam Husain (a.s) wanda shi ne Imami na 3 na iyalan gidan manzon Allah (a.s), tare da iyalansa da sahabbansa.

A madadin sashen Hausa Na Muryar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, muna taya dukkanin al'ummar musulmi juyayin wannan lokacin na zagayowar lokacin da Imam Husain (a.s) ya yi Shahada.