Shugaban Kasar Suizeland Zai Ziyarci Iran
A ziyara tasa ta kwanaki uku shugaba Johann Schneider zai gana da takwaransa na Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Suizeland Johann Schneider-Ammann zai fara wata ziyara aiki gobe Juma'a a birnin Tehran na Iran.
Ziyara ta Mr Schneider nada manufar kara dangantaka diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
A ziyara tasa ta kwanaki uku shugaba Johann Schneider zai gana da takwaransa na Iran Hassan Rohani, inda ake sa ran zasu tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi alakar kasashen biyu, kama daga kasuwanci, kimiya, zuba jari, masana'antu da dai sauran su.
A shakaru biyu da suka gabata kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar fitar da iskar gas din Iran zuwa kasar Suizeland har zuwa Turai, saidai basu kaima cimma wannan gurin ba.