A Gobe Al'ummar Iran Ke Zaben 'Yan Majalisa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i1273-a_gobe_al'ummar_iran_ke_zaben_'yan_majalisa
Offishin ministan cikin gida na kasar Iran ya sanar cewa komi ya kammala a shirye-shiyen zaben 'yan majalisar dokoki dana kwararu da za'a gudanar gobe juma'a idan Allah ya kai.
(last modified 2018-08-22T06:57:51+00:00 )
Feb 25, 2016 12:45 UTC
  • A Gobe Al'ummar Iran Ke Zaben 'Yan Majalisa

Offishin ministan cikin gida na kasar Iran ya sanar cewa komi ya kammala a shirye-shiyen zaben 'yan majalisar dokoki dana kwararu da za'a gudanar gobe juma'a idan Allah ya kai.

Da yake bayani ga manema labarai ministan cikin gida na Iran Abdel-Reza Rahmani Fazli ya ce duk kayan da ake bukata domin gudanar da zaben an rigai anyi tanadin su, illah kawai fatan sa al'ummar kasar su fito dafifi domin kada kuri'ar su.

kimanin Iraniyawa miliyan 55 da suka cancanci kada kuri'a za suyi zaben domin zabar 'yan majalisar dokoki 290, gami da 'yan majalisar kwararun su 88.

kafin hakan dama shugaban kasar ta Iran Dr Hassan Rohani yayi kira ga daukacin bangarorin al'ummar kasar dasu fito dafifi a zaben wanda hakan zai kara nuna yadda tsarin demukuradiyya ya samu gindin zama a kasar.

Da Misalin karfe takwas na safiyar yau Alhamis ne aka kawo karshen yakin neman zaben.