Jagora: Duk Wanda Yake Son Iran Ya Fito Don Kada Kuri'arsa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i1300-jagora_duk_wanda_yake_son_iran_ya_fito_don_kada_kuri'arsa
A dazu dazun nan ne aka fara zaben majalisun dokoki da kuma naMajalisar Kwararru na zaben Jagora a duk fadin kasar Iran.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 26, 2016 02:02 UTC
  • Jagora: Duk Wanda Yake Son Iran Ya Fito Don Kada Kuri'arsa

A dazu dazun nan ne aka fara zaben majalisun dokoki da kuma naMajalisar Kwararru na zaben Jagora a duk fadin kasar Iran.

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khamina ya kada kuri'unsa a rumfan zabe mai lamba 110 da ke cikin Husainiyyar Imam Khomaini(a) da misalign karfe 8 da minta goma.

Bayan kada kuri'unsa Jagorar ya yi wata gajeruwar jawabi ga mutanen kasar Iran inda a ciki ya bayyana muhimmanci zaben na yau da kuma kodaitar da duk wadanda suke da son kasar su fito su kada kuri'unsu.

Jagoran ya bayyana cewa zabe wani aiki ne na alkhairi. Sannan addinin musulunci ya kodaitar da musulmi su gaggauta zuwa aikata aikin alkhairi.

Mutanen kasar Iran wadanda suka cancanci kada kuri'a kimani million 55 ne aka saran zasu fito konsu da korkotansu don zaben wakilan majalisar dojojin kasar Iran 290 da kuma wakilai a majalisar kwararru 88.

Mohammad Hossein Moqimi , shugaban bangaren zabe na ma'aikatar cikin gida ya ce suna da akwatunan zabe dubu 120,000 a duk fadin kasar. Sannan yan takara dubu 4,844 ne , 500 daga cikinsu mata suke suke takara shiga majalisar dokokin kasar.