Limamin Tehran: Wajibi ne ga Musulmi Su Hada Kai Domin Fuskantar Makiyansu.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i13051-limamin_tehran_wajibi_ne_ga_musulmi_su_hada_kai_domin_fuskantar_makiyansu.
Hadin Kan Musulmi Wajibi Ne Domin Fuskantar Makiya
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 28, 2016 15:25 UTC
  • Limamin Tehran: Wajibi ne ga Musulmi Su Hada Kai Domin Fuskantar Makiyansu.

Hadin Kan Musulmi Wajibi Ne Domin Fuskantar Makiya

Wanda ya jagoranci sallar juma'a a nan Tehran ya ce: Wajibi ne ga musulmi da su hada kawukansu domin tsayin daka wajen fuskantar makiyan addininsu.

Ayatullah Muhammad Imami Kashani, ya bayyana cewa; Wajibi ne ga musulmi su zama cikin fadaka su kuma hada kai domin kalubalantar wadanda su ke son rusasu.

Ayatullah Muhammad Imami Kashani ya ci gaba da cewa; Daya daga cikin manufofin makiya shi ne raba musulmi da koyarwar addininsu, sanann ya kara da cewa: Domin cimma wannan manufar  ta makiya suna kokarin fassara musulunci ta hanyoyi daban-daban.