Sallar Juma'a A Tehran
Limamin Tehran Ya Jinjinawa Fitowar Mutane A Zaben 'Yan Majalisa
Wanda ya jagoranci sallar juma'a anan Tehran, Hujjatul-Islam Wal Muslimin, Kazim Siddiqy ya bayyana gamsuwa akan yadda ake gudanar da zabe cikin nutsuwa da tsaro sanann ya kara da cewa; Al'ummar Iran sun sake fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kare juyin juya halin musulunci."
Limamin na Tehran ya kuma yi ishara da kokarin da makiya su ke yi domin samun kofar shiga a harkokin cikin gidan Iran, musamman bayan cimma yarjejeniyar Nukiliya, sai ya ce; Wanzuwar tsarin jamhuriyar musulunci na Iran yana tattare ne da fitowar mutane domin domin ayyana makomar Iran da kuma ci gaban tsarin musulunci da jagorancin malami.
Hujjatul-Islam Saddiqy ya kuma ce; Ya kamata makiya su sani cewa kawo ya zuwa yanzu al'ummar Iran ba su shiga karkashin ikon wani karfi na waje ba, ba kuma za su yi wa makiya mubaya'a ba.