Shugaban Kasar Swissland Ya Iso Tehran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i1327-shugaban_kasar_swissland_ya_iso_tehran
Shugaban Kasar Swissland Ya Fara Ziyarar Aiki A Iran
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 26, 2016 15:29 UTC
  • Shugaban Kasar Swissland Ya Iso Tehran

Shugaban Kasar Swissland Ya Fara Ziyarar Aiki A Iran

Shugaban Kasar Swissland da tawagar da ta ke yi masa rakiya sun iso Iran dazu, domin fara ziyarar aiki.

Kamfanin Dillancin Labarun Irna ya nakalto cewa; shugaban kasar Swissland Johann Schneider ya iso Tehran dazunan inda ya sami tarbar ministan masana'antu da ma'adanai na Iran, Muhammad Ridha Ni'imata Zadeh.

Gabanin barowarsa kasar Swissland, shugaba Johann Schneider ya fadawa manema labaru cewa; kasar tasa za ta zama abokiyar cinikayya da kasuwanci ta Iran.

A yayin ziyarar ta shugaban kasar Swissland da tawagar da ta ke yi masa rakiya, za kulla yarjeniyoyi masu yawa da Iran da su ka kunshi mu'amala da Bankuna da siyasa da kuma al'adu.

Alaka a tsakanin Iran da Swissland dai ta fara ne tun a karni na 17 miladiyya wacce ta kawo har yanzu.