Vilayati: Gwagwarmayar Fada Da Masu Girman Kai Tana Ci gaba.
Nov 15, 2016 08:36 UTC
Amurka ba za ta iya jan daga da Iran ba.
Shugaban Cibiyar nazari da bincike akan muhimman dabarun siyasa, da ke karkashin majalisar kare maslahar musulunci ta Iran, ya ce; Gwagwarmaya da manyan kasashe masu girman kai da su ka hada da Amurka yana ci gaba.
Ali Akbar Vilayaty, ya ci gaba da cewa; Idan Amurkawa ta san cewa za ta iya lakume jamhuriyar musulunci ta Iran, to da ba ta zauna kan tuburin tattaunawa da ita ba.
Ali Akbar Vilayaty ya ci gaba da cewa; Ko kadan Amurka ba za ta iya jan daga da jamhuriyar musulunci ta Iran ba.