Iran Ta Mayar Da Martani Kan Zarge-Zargen Sarakunan Larabawa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i15010-iran_ta_mayar_da_martani_kan_zarge_zargen_sarakunan_larabawa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani kan bayanin bayan taron sarakunan larabawan kasashen yankin tekun Fasha da ke zargin Iran da shiga cikin harkokin kasashen larabawa.
(last modified 2018-08-22T06:59:22+00:00 )
Dec 08, 2016 14:10 UTC
  • Iran Ta Mayar Da Martani Kan Zarge-Zargen Sarakunan Larabawa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani kan bayanin bayan taron sarakunan larabawan kasashen yankin tekun Fasha da ke zargin Iran da shiga cikin harkokin kasashen larabawa.

Kakakin maaikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Kasimi ya bayyana cewa, taron sarakunan larabawan bai zo da wani sabon abu ba in banda maimata tuhumar da suka saba yi a owace sheakara a kan Iran, kan cewa tana shiga cikin harkokinsu.

Ya ce kasarsa ba ta shiga cikin harkar wata kasa, kuma babban kure ne yadda sarakunan suka mayar da batutuwa na siyasa  amatsayin makamin rarraba kan al'ummar musulmi da sunan banbancin mazhaba ko fahimta ta addini, wanda hakan abbu abin da zai sai kara tarwatsa al'ummar musulmi da hada su yake-yake kamar yadda kowa yake gani a halin yanzua  kasashen larabawa.

Dangane da kalaman da Firayi ministan kasar Birtaniya Theresa May ta yi a wurin taron kuwa, da ke cewa Birtaniya za ta hada kai da sarakunan larabawa domin kalubalantar Iran, Kasimi ya bayyana cewa, irin wadannan mutanne da suke zuwa daga wajen yankin su ne suke kara zuzuta wutar riki a tsakanin kasashen musulmi, abin ban takaici kuma shi ne yadda musulmin suka mika musu wuya kamar rakumi da akala.

Kasimi ya ce kowa ya san abin da ya kawo Theresa May a wurin taron sarakunan larawa, shi ne batun cinikin makamai na biliyoyin dalolin da suke sayar musu, domin ci gaba da rusa kasashen larabawan, babban misalin hakan shi en abin ke faruwa a Syria, Iraki, Bahrain da kuma Yemen, inda sarakunan larabawan ne suke yakar al'ummomin wadandannan kasashe da kansu ko kuma ta hanyar tura 'yan ta'adda.