Allah Ya Yi Wa Ayatollah Hashimi Rafsanjani Rasuwa A Yammacin Yau
Da yammacin yau ne Allah ya yi shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci ta Iran Ayatollah Akbar Hashimi Rafsanjani rasuwa.
Ayatollah Rafsanjani ya rasu ne a wani asibiti da ke nan birnin Tehran a yammacin yau, sakamakon matsalar zuciya.
Sheikh Rafsanjani ya rasu yana da shekaru 83 a duniya, ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yi gwagwarmayar kafa juyin juya halin muslunci a Iran a karkashin jagorancin marigayi Imam Khomenei, haka nan kuma ya fuskanci azabtarwa a gidan kurkukun sarki Shah.
Bayan samun nasarar juyin juya halin mulsunci a shekara ta 1979 a kasar Iran, Sheikh Rafsanjani ya rike mukamai da dama, daga ciki kuwa har mukamin shigaban kasa, shugaban majalisar dokoki ta kasa, shugaban majalisar kwararru masu zaben jagora, ya kuma rasu yana rike da mukamin shugaban majlisar fayyace maslahar tsarin muslunci.