Shamkany: Iran Za ta Kalubalanci Tsoma Bakin Kasashen Waje Akan Harkokin Tsaronta
(last modified Thu, 02 Feb 2017 06:27:59 GMT )
Feb 02, 2017 06:27 UTC
  • Shamkany: Iran Za ta Kalubalanci Tsoma Bakin Kasashen Waje Akan Harkokin Tsaronta

Babban sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Ya ce: Duk wani tsoma baki da wata kasar waje za ta yi akan gwajin makamai masu linzami na Iran, to a ta fuskanci maida martani

Babban sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya ce: Duk wani tsoma baki da wata kasar waje za ta yi akan gwajin makamai masu linzami na Iran, to a ta fuskanci maida martani.

Ali Shamkhani da ya ke magana a jiya laraba da ya gana da ministan tsaron kasar Armenia  Vigen Sargsyan ana Tehran, ya ce;  Jamhuriyar Musulunci ba ta bukatar izinin wata kasa domin bunkasa karfinta na tsaro.

Shamkhani ya kuma yi ishara da yadda kasashen yammacin turai su ke amfani da ta'addanci a matsayin makamin fada da wasu kasashe kamar Iran da kuma Syria, sannan kuma ya bayyana cewa: Alakar da ta ke tsakanin Iran da kasar Armenia, wajibi ne a bunkasa ta, musamman ma dai ta fuskar tsaro.

Bugu da kari, babban magatakardan majalisar koli ta tsaron kasar Iran din ya kuma ce; Kyautatawa makwabta yana daga cikin ginshikan siyasar waje ta jamhuriyar musulunci ta Iran.

Har ila yau, Shamkhani ya jaddada cewa; Iran za ta ci gaba da fada da ta'addanci a cikin kasashen Syria da kuma Iraki domin ganin an sami zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Ministan tsaron Armenia Vigen Sargsyan yana ziyarar aiki ne ta kwanaki uku a Iran.