Shamkhani: Mahukuntan Saudiyya Sun Taka Gagarumar Rawa A Fagen Goyon Bayan Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i18082-shamkhani_mahukuntan_saudiyya_sun_taka_gagarumar_rawa_a_fagen_goyon_bayan_ta'addanci
Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai taba mancewa da irin gagarumar rawar da mahukuntan Saudiyya suka taka a fagen samar da kungiyoyin 'yan ta'adda tare da goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:45+00:00 )
Feb 27, 2017 14:32 UTC
  • Shamkhani: Mahukuntan Saudiyya Sun Taka Gagarumar Rawa A Fagen Goyon Bayan Ta'addanci

Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai taba mancewa da irin gagarumar rawar da mahukuntan Saudiyya suka taka a fagen samar da kungiyoyin 'yan ta'adda tare da goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya ba.

A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Tehran a yau Litinin: Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewa; Mahukuntan Saudiyya sun taka gagarumar rawa a fagen goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya musamman a kasashen Iraki da Siriya lamarin da ya janyo munanan hatsarori na rayuka da na dukiyoyi, don haka tarihi ba zai taba mancewa da irin wannan barna ba.

A tsokacinsa dangane da ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ya kai zuwa kasar Iraki: Ali Shamkhani ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana daukan matakin da duk wata kasa da tayi fice a fagen goyon bayan ayyukan ta'addanci musamman Saudiyya zata dauka na canza siyasarta domin gyara barnar da tayi a baya, da muhimmanci amma har yanzu a fili yake mahukuntan Saudiyya basu canza dabi'arsu ba saboda babu wani abin da suka aikata da ke nuna nadama kan muggan laifukan da suka tafka a baya.

Ali Shamkhani ya kara da jaddada cewa: Duk wani nau'in horo da za a bai wa 'yan ta'adda matukar aka samu cibiyar tsaron kasa mai basira da al'umma masu fadaka, to babu wani tasirin da 'yan ta'adda zasu yi a kasar kuma sakamakon haka ne dukkanin makirce-makircen da makiya suke shiryawa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka kasa cimma nasara.