Iran: Tattaunawar Syria tana dauke da cusa fata.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce; Gwarwgadon yadda gwamnati da yan hamayya su ke tattaunawa ake kara samun kyakkyawan fata.
Bahram Qasimi wanda ya gabatar da taron manema labaru a nan birnin Tehran, ya bada jawabi akan tambayar da aka yi masa dangane da taron Geneva akan Syria, ya ce; Tattaunawar tana ci gaba da tafiya kamar yadda ya ce; kamar yadda tattaunawar Astana ta kasance.
Kakakin ma'aikatar harkokin Wajen kasar ta Iran ya kuma tabo batun rikicin kasar Bahrain inda ya ce; Abubuwan da su ke faruwa sun shafi cikin gidan kasar ta Bahrain ne.
Kasimi ya kara da cewa; masu mulki a kasar ta Bahrain sun kasa warware matsalar da kasar ta ke ciki, don haka su ke dorawa jamhuriyar musulunci ta Iran duk wani abu da ya ke faruwa.