Martanin Iran kan kasar Turkiya
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da tuhumce-tuhumce "marasa tushe" da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyip Erdogan yayi mata tana mai cewa Turkiyya tana zargin wasu kasashe na daban ne don ta rufe da kuma halalta bakar siyasarta ta neman mulkan sauran al'umma.
A yayin da yake mayar da martani kan kalaman Shugaba Erdogan na kasar Turkiya, Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qassemi ya bayyana cewa jami'an kasar Turkiyya suna kokarin halalta irin baki cikin harkokin wasu kasashe da suke yi da kuma siyasarsu ta mulkin mallaka ne ta hanyar ci gaba da zargin wasu kasashe na daban.
Har ila yau kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kirayi jami'an kasar Turkiyya da su guji irin wadannan tuhumce-tuhumce marasa tushe kana kuma su yi kokari wajen girmama mutumci da ikon da kasashe da suke makwabtaka da su musamman kasashen Iraki da Siriya inda Turkiyya take ci gaba da taka gagarumar rawa wajen dagula lamurran tsaro a wadannan kasashe ta hanyar taimakon kungiyoyin 'yan ta'addan da suke yaki a can.
Qassemi ya ce ikrarin da magabatan Turkiya ke yi na cewa sama da Iranawa million uku ne suka bi ta kasar domin neman mafuka a kasashen Turai, zarki ne maras tushe,sama da shekaru 30 da suka gabata, kasar Iran ta karbi bakuncin milyoyin 'yan kasashen dake makobtaka da ita, kuma kamata yayi magabatan na Turkiya su dauki darasi daga kasar Iran, saboda cimma wata manufar Siyasa ta musaman ga wasu kasashe, bai kamata magabatan Turkiyan su dinga sukan wasu kasashe ba.
Magabatan kasar Turkiyan sun karbi bilyoyin daloli daga kungiyar Kasashen Turai, bayan alkawarukan da ta sanya hannu kansa na taimakon 'yan gudun hijra da kuma rage kwararar su zuwa kasashen Turai, a cikin wasu kasashen Turai, kasar Turkiya ta fuskanci kalu bale dangane da manufofin ta inda aka hana 'yan kasar ta, gudanar da farfagandar zaben jin ra'ayin al'umma na canza kundin tsarin milkin kasar,a halin da ake ciki, Dubun dubutan 'yan kasar Turkiya ne suka bukaci neman mafuka a kasashen na Turai, Jaridar Der Tagesspiegel ta kasar Jamus ta habarta cewa a shekarar da ta gabata Turkawa 5742 ne suka bukaci mafuka a Ofishin Jakadancin kasar Jamus dake birnin Ankara, a nata bangare,Ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra ta kasar Girka ta habarta cewa daga watan Janairun 2016 zuwa watan Favrayun 2017, Turkawa 236 ne suka bukaci mafukar siyasa a kasar. baya ga wannan mas'ala, daukan wannan matsayi na magabatan kasar Turkiya na zuwa ne a yayin da Sojojin kasar suka kasa a kasar Siriya, da kuma yadda magabatan hukumar 'yan gudun hijra ta MDD ke yabon kasar Iran , kan yadda ta dauki bakuncin milyoyin 'yan gudun hijra a cikin 'yan shekarun nan.
A Ranar Asabar din da ta gabata ce shugaban kasar Turkiyyan, a yayin wani jawabi da yayi a garin Antalya da ke kudancin Turkiyya ya zargi Iran da gudanar da siyasar wariya a kasar Iraki. Erdogan yana wannan maganar ne a daidai lokacin da gwamnatin Iraki take zargin gwamnatinsa da aikata irin wannan siyasar a kasar da kuma taimakon 'yan ta'addan a kasar Irakin.