Rasha: Iran Tana Yaki Da Ta'addanci A Yankin Gabas Ta Tsakiya
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana kasar Iran a matsayin kasar da take yaki da ta'addanci a yankin gabas tsakiya.
Sergie Lavrov ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi da mujallar National Interest ta kasar Amurka, inda ya bayyana cewa Iran tana da babban tasiri a yankin gabas ta tsakiya, kuma tana yaki da ta'addanci a yankin, kuma Rasha tana yin aiki na hadin gwiwa tare da Iran a wannan bangare, domin wanzar da sulhu da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Dangane da kungiyar Hizbulla da kuma rawar da take takawa kuwa, ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa; kungiyar Hizbullah tana taka gagarumar rawa a fagen yaki da 'yan ta'adda, a daiai lokacin da gwamnatin Amurka da wasu daga cikin gwamnatocin larabawa na yankin suke ta hankoron ganin ganin sun taimaka ma 'yan ta'addan.