Limamin Juma'a: Iran Za ta Maida Martani AKan kowace Irin Barazana.
Wanda ya jagoranci Sallar Juma'a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran za ta maida martani akan kowace irin baraza da karfi.
Wanda ya jagoranci Sallar Juma'a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran za ta maida martani akan kowace irin baraza da karfi.
Limamin Juma'ar ya kuma yi ishara da shirin da kasashen turai su ka kirkiro na cuwa kin jinin Iran, sannan ya kara da cewa: Kin jinin Iran a cikin kasashen turai da kuma wasu kasashen larabawa da gabas ta tsakiya, ba sabon abu ne, kuma dalilinsa shi ne tafiyar da tsarin musulunci da kuma adalci a cikin Iran.
Limamin na Tehran ya kuma ambato laifukan da Saudiyya ta ke tafkawa akan al'ummar kasar Yemen da ba su ji ba su gani ba, sannan ya ce; Aikewa da makamai da Amurka da kasashen turai su ke yi zuwa ga Saudiyya da kuma shirun da kungiyoyin kasa da kasa su ke yi, su ne dalilan ci gaba da kashe mutanen na Yemen.
Ayatullah Khatami ya bayyana cewa; Ranar 12 ga watan Farvardin da ita ce Ranar Jamhuriyar musulunci, a rana irin wannan a 1979, al'ummar Iran sun kada kuri'ar raba gardama da su ka zabi tsarin jamhuriyar musulunci.
Har ila yau, limamin ya yi ishara da manyan zabuka na shugaban kasa da na 'yan majalisa da za a yi a ranar 19 ga watan Mayu na 2017, sannan ya ce fitowar mutane yana da matukar muhimmanci.