Amurka Ta Ce Tana Sake Nazari Kan Siyasarta Dangane Da Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19630-amurka_ta_ce_tana_sake_nazari_kan_siyasarta_dangane_da_kasar_iran
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa gwamnatin Amurka tana tunanin sake nazari kan siyasarta da suka shafi Jumhuriyar Musulunci ta Iran.
(last modified 2018-08-22T06:59:59+00:00 )
Apr 20, 2017 10:34 UTC
  • Amurka Ta Ce Tana Sake Nazari Kan Siyasarta Dangane Da Kasar Iran

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa gwamnatin Amurka tana tunanin sake nazari kan siyasarta da suka shafi Jumhuriyar Musulunci ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Rex Tillerson yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa yerjejeniyar nuclear tsakanin Iran da kasahe 5+1 wani kuskure ne babba wanda gwamnatin Amurka da ta shoode ta aiwatar. 

Rex Tillerson ya kara da cewa wannan kuskuren da gwamnatin Obama ta yi ta bawa Iran dama ce na ta mallaki makaman Nuclia.

A shekara ta 2015 ne dai kasahe 5 masu kujerun din din din a Majalisar dinkin duniya tare da kasar Jamus suka cimma yerjejeniya da kasar Iran kan shirinta na makamacin Nuklia, inda ta amince ta takaita shirin na wani lokaci don wadanda kasashe su sassauta mata takunkuman da suka dora mata.

Har ya zuwa yanzu dai hukumar IAEA da Majalisar dinkin duniya sun tabbatar da cewa gwamnatin kasar Iran tana kiyaye alkawuran da ta dauka a wannan yerjejeniyar.