Mahalarta Gasar Alkur'ani Mai Girma Sun Gana Da Jagora
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19872-mahalarta_gasar_alkur'ani_mai_girma_sun_gana_da_jagora
Malimai, makaranta tare da zababbu daga cikin Hafizan da suka halarci gasar Alkur'ani mai girma karo na 34 a nan birnin Terhan, A safiyar Yau Alkhamis sun gana da jagoran juyin juya halin musulinci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
(last modified 2018-08-22T07:00:01+00:00 )
Apr 27, 2017 13:49 UTC
  • Mahalarta Gasar Alkur'ani Mai Girma Sun Gana Da Jagora

Malimai, makaranta tare da zababbu daga cikin Hafizan da suka halarci gasar Alkur'ani mai girma karo na 34 a nan birnin Terhan, A safiyar Yau Alkhamis sun gana da jagoran juyin juya halin musulinci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A ranar Laraba19 ga watan Avrilun da muke ciki ne aka fara gasar Alkur'ani mai girma karo ta 34 bisa taken Al'umma daya Littafi daya tare kuma da halartar baki makarantar Alkur'ani mai girma kimanin 400 da suka fito daga kasashen Duniya 83 a nan birnin Tehran.

َA yayin ganawar, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokari wajen yada fahimtar Alkur'ani na daga cikin kyawawen aiyuka, domin haka ya bukaci mahalartan da su ci gaba da kokarin da suke yi na yada fahimta gami da koyar Alkur'ani mai tsarki,saidai abin bakinci shi ne da dama daga cikin kasashen musulinci sun yi nisa da koyar Alkur'ani mai tsarki na gaskiya.

Jagora ya kara da cewa kafircewa Dagutu da kuma Imani da Allah madaukakin sarki, misali ne na kyakkyawar fahimtar Alkur'ani mai girma, tabbatuwa a kan imani ga Allah ba shi ke nuna yaki ko kuma rashin alaka da shi ba, saidai abinda yake nufi samun 'yanci da 'yantuwa daga kangin bautar Dagutu.

Har ila yau, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kangin da Al'ummar musulmi ke ciki a yau, sakamakon mumunar siyasa da kuma riko da Al'adun yamma ne,da dama daga cikin kasashen musulmi ba su da fuskar shugabancin musulinci ko da kuwa Al'ummar kasashen na salla da azumi, rashin hadin kai da kuma nisa da kyakkyawar fahimtar Alkur'ani shi ne ya janyo  matsin tattalin arziki da kuma matsaltsalun da kasashen musulmi ke fuskanta a Yau.