Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadan Pakistan Da Ke Tehran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19896-ma'aikatar_harkokin_wajen_iran_ta_kirayi_jakadan_pakistan_da_ke_tehran
Ma'ikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadan kasar Pakistan da ke Tehran, domin nuna rashin jin dadi dangane da kisan da wasu 'yan ta'adda daga cikin Pakistan suka yi wa jami'an tsaron Iran masu gadi a kan iyakokin kasar da Pakistan.
(last modified 2018-08-22T07:00:02+00:00 )
Apr 28, 2017 12:28 UTC
  • Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadan Pakistan Da Ke Tehran

Ma'ikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadan kasar Pakistan da ke Tehran, domin nuna rashin jin dadi dangane da kisan da wasu 'yan ta'adda daga cikin Pakistan suka yi wa jami'an tsaron Iran masu gadi a kan iyakokin kasar da Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Kasimi ya fadi a yau cewa, an kirayi jakadan na kasar Pakistan domin nuna rashin gamsuwa da yadda Pakistan take gudanar da tsaro a kan iyakokinta da Iran, wanda hakan ne ya bai wa wasu 'yan ta'adda daga cikin kasar ta Pakistan damar kai hari a kan jami'an tsaro Iran a kan iyaka, tare da kashe 10 daga cikinsu.

Kasimi ya ce 'yan ta'addan sun yin harbi ne  a kan jami'an tsaron Iran daga cikin kasar Pakistan, kuma bayan kashe jami'an na Iran sun shige a cikin kasar ta Pakistan, a kan Iran na jiran ganin pakistan ta dauki matakin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, tare da zartar musu da hukuncin da ya dace da su.

A nasa bangaren jakadan Pakistan a Iran ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma al'ummar Iran, tare da nuna rashin jin dadi kan abin da ya faru, kamar yadda ya yi alkawalin mika sakon ma'aikatar harkokin wajen Iran ga gwamnatin kasarsa.