Iran Ta Ruguza Kungiyoyin 'Yan Ta'adda 30 A Shekarar Da Ta Gabata
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20102-iran_ta_ruguza_kungiyoyin_'yan_ta'adda_30_a_shekarar_da_ta_gabata
Ministan Tattara bayyanan Sirri na Jumhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa A shekarar da ta gabata jami'an leken asirin kasar sun samu nasarar dakile tare kuma ruguza kungiyoyin 'yan ta'adda 30 da suka kudirin kai hare-haren ta'addanci a wurare daban daban na kasar Iran
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
May 05, 2017 13:16 UTC
  • Iran Ta Ruguza Kungiyoyin 'Yan Ta'adda 30 A Shekarar Da Ta Gabata

Ministan Tattara bayyanan Sirri na Jumhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa A shekarar da ta gabata jami'an leken asirin kasar sun samu nasarar dakile tare kuma ruguza kungiyoyin 'yan ta'adda 30 da suka kudirin kai hare-haren ta'addanci a wurare daban daban na kasar Iran

Cikin wani jawabi da ya gabatar gabanin sallar Juma'a a yau,Ministan Tattara bayyanan sirri na jumhoriyar musulinci ta Iran Hujjatul-islam wal musulimin Sayyid Mahmud Alawy ya kara da cewa a shekarun 1393 da kuma 1394 hijra Shamsiya wato shekarun 2014 da kuma 2015 miladiya  jami'an leken asirin kasar sun samu nasarar ruguza kungiyoyin 'yan ta'adda kimanin 45.

Minstan ya ce baya ga hakan jami'an Leken asirin sun samu nasarar gano makamai masu yawa a wajen 'yan ta'addar daga ciki akwai wasu nau'in bama-bamai na mayan karfe 108 da kuma irin nau'in jakar da 'yan ta'adda ke amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake 15.

Sayyid Mahmud Alawy ya tabbatar da cewa Ma'aikatar tattara bayyanan sirri ta kasar nada cikekken bayyanan a kan duk wani kokarin da makiya ke yi na kawo cikas ga zaman lafiya da kuma tsaron kasar.

Har ila yau Ministan tattara bayyanan sirri na kasar ta Iran ya kara da cewa  kwararru masu kiro da addini daga cikin jami'an leken asirin kasar ta Iran na aiki dare da rana domin tabbata da tsaro a kasar kuma wannan sanannan abu ne a ciki da wajen kasar.