Sharhi: Jan Kunnen Iran Dangane Da Barazanar Ministan Tsaron Saudiyya Ga Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20200-sharhi_jan_kunnen_iran_dangane_da_barazanar_ministan_tsaron_saudiyya_ga_iran
Tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon ta jiyo ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan yana fadin cewa matukar dai gigi ya debi Saudiyya ta kawo wa Iran hari, to kuwa baya ga garuruwan Makka Da Madina, babu wani waje a Saudiyyan da zai tsira.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 09, 2017 01:14 UTC
  • Sharhi: Jan Kunnen Iran Dangane Da Barazanar Ministan Tsaron Saudiyya Ga Iran

Tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon ta jiyo ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan yana fadin cewa matukar dai gigi ya debi Saudiyya ta kawo wa Iran hari, to kuwa baya ga garuruwan Makka Da Madina, babu wani waje a Saudiyyan da zai tsira.

Ministan tsaron na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar ta Al-Manar a matsayin mayar da martani ga kalaman ministan tsaron Saudiyya kana kuma yariman yarima mai jiran gado na kasar Muhammad bn Salman a kwanakin baya inda yayi barazanar kaddamar da yaki har zuwa kan iyakokin Iran inda ya ce: matukar dai gigi ya debi Saudiyya ta kawo wa Iran hari, to kuwa baya ga garuruwan Makka Da Madina, babu wani waje a Saudiyyan da zai tsira.

Birgediya Janar Dehqan ya kara da cewa girman kan jami'an kasar Saudiyya shi ne yake sa su fadin wasu maganganu da su kansu ba su fahimci hatsarinsa ba. Babban abin da kawai za su iya shi ne hada baki da haramtacciyar gwamnatin Sahyoniyawa a kan Iran. Ministan ya kara da cewa a halin yanzu dai duniya ta ga yadda mahukuntan Saudiyya suka zamanto wasu 'yan amshin shatan Netanyahu.

Tsawon tarihi dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kokari mamaya ko kuma wuce gona da iri kan wata kasa ta daban ba, to amma a lokuta da dama ta sha bayyana cewar ba za ta taba yin kasa a gwuiwa ba wajen mayar da martani mai kaushin gaske ga duk wani da yayi kokarin wuce gona da iri a kanta. Wannan wata siyasa ce da Iran din ta dauka da babu ja da baya kanta.

Abin bakin cikin shi ne cewa kasar Saudiyya wacce ita ce ummul aba'isin matsalar da yakukuwa, rikice-rikice da tsaurin ra'ayi da ayyukan ta'addancin da yankin Gabas ta tsakiya da sauran kasashen musulmi suke fuskanta a halin yanzu, maimakon ta yi tunanin magance wannan kuskure nata; a halin yanzu kuma ta koma tana barazana ga Iran; barazanar da da dama suke ganin ta wuce irin matsayi da karfin da take da shi. Sabanin mahukuntan Saudiyyan da suka gabata wadanda suke yin taka tsantsan cikin mu'amalarsu da kasashen yankin nan, su kuwa sabbin mahukuntan na yanzu kokari suke yi wajen sun tilasta ra'ayinsu ga sauran kasashen yankin. Babbar manufar sabbin mahukutan Saudiyyan karkashin jagorancin dan sarkin kuma ministan tsaron kasar Muhammad bn Salman ita ce tabbatar da ikonsu a kan kowa ta kowace hanya. Kara karfafa kasantuwar sojojin Saudiyya a Bahrain da nufin diran mikiya kan 'yan Shi'an kasar, ci gaba da yakin wuce gona da iri a kasar Yemen, abin da ya faru ga maniyyata a Mina, zartar da hukuncin kisa a kan Shehin malamin kasar Sheikh Nimar wasu ne daga cikin irin wannan siyasa ta sabbin mahukutan Saudiyyan.

Hakan ne ma ya sanya Muhammad bn Salman din yin dukkanin abin da zai iya ciki kuwa har da hada baki da Amurka, Birtaniyya da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila don cimma wannan bakar aniya ta su, wanda daga karshe babban sakamakon hakan shi ne karfafa haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kawar da duk wata barazana da ka iya fuskantarta.

To sai dai abin da yake a fili wanda kuma ita ce hakikanin lamarin shi ne cewa kasar Saudiyya ba ta da karfin da za ta iya cimma wannan manufa nata; don kuwa ba ita ba hatta su kansu wadannan manyan kasashen duniyan da take dogaro da su din suna cikin tsaka mai wuya a wannan fagen. To sai dai wani abu da ya kamata mahukutan Saudiyyan su fahimta musamman dangane da wannan siyasa ta su ta barazana ga tsaro da zaman lafiyan Iran din shi ne abin da ministan tsaron na Iran ya fadi cikin wannan hira da yayi da tashar ta Al-Manar. Ya kamata su fahimci matsayinsu da kuma abin da za su iya yi. Su fahimci cewa hatta Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ilan ba su da karfin gwiwan kawo wa Iran hari, don kuwa sun san abin da zai iya samunsu matukar suka bari gigi ya debe su.