Shugaba Ruhani Ya Taya Al'ummar Musulmi Murna Na Shiga Watan Ramadana
Shugaban Kasar Jumhoriyar Musulinci ta Iran Dakta Hasan Ruhani ya taya Kasashen musulmi murna na shiga watan Ramadana mai alfarma.
Cikin wani sako da ya aikewa Shugabanin kasashen musulmi, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya taya Al'ummar musulmi murna na shiga watan Ramadana mai alfarma tare kuma da neman hadin kan musulmi wajen kalubalantar makiya kan yadda suke bayyana addinin islama ta hanyar tsoratar da Mutane.
Cikin Jawabin nasa, Shugaba Ruhani ya ce Shakka babu, nauyi da ya rataya a kan dukkanin masana da maliman Addini na kasashen musulmi cikin wannan wata mai alfarma, watan Rahama da neman gafarar Ubangiji su bayyana wa Al'umma Hakikanin manufar Addinin Islama a aikace da kuma kalubalantar irin makirci da kuma batanci da makiyansa suka kirkiro domin sanya tsaro da kwada Addinin a matsayin Addinin ta'addanci.
Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana fatansa a cikin wannan wata mai albarka, a kan dukkanin musulmin Duniya da su rabauta da Albarka gami da alkhairan dake cikin sa tare da taimakon juna da kuma shuguwa a tsakanin su wacce ta fi ta shekarun da suka gabata, kuma ya bukaci tsaro da sulhu ya dawo a kasahsen musulmi na Duniya.