Limamin Juma'a:Riko Da Musulinci Shi Ne Sirrin Cin Nasarar Iran
Limamin da ya jagoranci Sallar Juma'a a nan Birnin Tehran ya bayyana cewa Amurka ita ce babbar makiyar Al'ummar Iran amma riko da musulinci , Alkur'ani da kuma jumhoriyar Musulinci zai sanya a kalubalanci Amurka da duk wasu Makiya.
A yayin da yake bayyani kan amfanin Al'ummar Iran Ayatollahi Muhamad Ali Muwahidy Kermany Limamin da ya Jagoranci Sallar Juma'a ta nan birnin Tehran ya ce Hakan na tabbatuwa ne a yayin da manufofin Al'ummar kasar bai yi karo da juna ba, rashin dogaro da makiya da kuma amfani da Matasan kasar gami da juriya a kan matsin lambar tattalin arziki daga makiya ita ce hanya guda cilo da zai a kai ga gaci da kuma tsayawa a gaban makiya.
Ayatollahi Kermany ya kara da cewa Amurka ita ce babbar makiyar mu, domin haka kadda mu yaudaru da makircin makiya, kadda mu kasance masu tsammanin wani abu na alheri daga gare ta, kuma bai kamata ba muyi dogaro da Amurka, matukar dai mun kasance masu riko da tsarin Jumhoriyar musulinci, masu goyon bayan jumhoriyar Musulinci, masu goyon bayan musulinci, masu riko da Alkur'ani, matukar dai kuma mun kasance masu riko da tafarkin iyalan gidan Anabta tsarkaka, kadda muyi tsammanin murmushi daga mahukuntan Amurka, ko da kuwa sun yi mana murmushin to shakka babu karya suke yi, suna so ne su yaudare mu.
A yayin da ya koma kan magabatan kasar, Ayatullahi Muwahidi Kermany ya bukace su da suka kasance masu karbar laifi kuma su gyara, su kuma mayar da hankalin su wajen shafe hawayen Tallakawa,kuma su sake Nazari kan yadda Shugaban Muminai Aliyu bn Talib (a.s) ya zabi Magabata da kuma yadda ya raba dukiyar baitul-mali a yayin hukumar musulinci da ya jagoranta.