Iran: Yin Kira Da A Fito Domin Raya Ranar Kudus Ta Duniya
Ma'aikatar al'adu da shiryarwar musulunci ta Iran ta gayyaci al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin raya ranar kudus da ta duniya.
Ma'aikatar al'adu da shiryarwar musulunci ta Iran ta gayyaci al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin raya ranar kudus da ta duniya.
Kamfanin dillancin labarun "Irna' na Iran ya ambato sanarwar da aka fitar a yau talata da ta kunshi cewa; " Palasdinu ce wurin da aka saukarwa da annabawa wahayi kuma cibiyar addinan da Allah ya saukar, kuma albarka tana kewaye da ita ta ko'ina. Bugu da kari Palasdinu wani yanki ne na tarihin wannan al'umma, kuma alkiblar musulmi ta farko."
A ranar juma'ar karshe ta kowane watan Ramadan ce ake raya ranar kudus ta duniya wacce Imam Khumain ya ayyana, a cikin Iran da kuma duniyar musulmi baki daya.