Iran: Amurka Tana Wasa Da Wuta A Kasar Syria
(last modified Wed, 28 Jun 2017 18:59:49 GMT )
Jun 28, 2017 18:59 UTC
  • Iran: Amurka Tana Wasa Da Wuta A Kasar Syria

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce; Halayyar da Amurka ta ke nunawa a kasar Syria da babu tunani a ciki, shi ne wasa da wuta.

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce; Halayyar da Amurka ta ke nunawa a kasar Syria da babu tunani a ciki, shi ne wasa da wuta.

Ali Shamkhani wanda ya ke maida martani akan barazabar da Amurka ta ke yi wa Syria akan cewa; wai Syria tana shirin amfani da makamai masu guba, ya jaddada cewa; Sake bijiro da wannan batun wanda ba shi da wani tushe, yana nuni ne da cin kasar da masu fada da sojojin Syria su yi.

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya ci gaba da cewa; tun bayan harin baya da Amurka ta kai a shu'airat, wanda ya ginu akan shaci-fadi,  Iran da Rasha sun bukaci a tura masu bincike na kasa da kasa amma Amurkan ta hana ayi hakan.