Akwai Wahala A Cimma Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i22066-akwai_wahala_a_cimma_yarjejjeniyar_tsagaita_wuta_a_siriya
Kakakin Ma'aikatar Harakokin Kasashen wajen Iran ya ce matukar Amurka ba ta dakatar da fadanta kan Siriya ba to akwai wahala a cimma yarjejjeniya tsagaita wuta a kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:21+00:00 )
Jul 10, 2017 07:13 UTC
  • Akwai Wahala A Cimma Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Siriya

Kakakin Ma'aikatar Harakokin Kasashen wajen Iran ya ce matukar Amurka ba ta dakatar da fadanta kan Siriya ba to akwai wahala a cimma yarjejjeniya tsagaita wuta a kasar

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da yarjejjeniyar da kasashen Rasha da Amurka suka cimma kan tabbatar da yarjejjeniyar tsagaita a Siriya , Bahram Kasimi kakakin Ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa ba za a yi bada tabbaci na zartar da yarjejjeniyar da aka cimma ba, saboda matukar kasar Amurka ba ta dakatar da kiyayya  da kuma fatan ta a kan Gwamnatin Siriya ba to da wahala a zartar da yarjejjeniyar.

Kasimi ya kara da cewa Kasashen Iran, Rasha da Turkiya na iya nasu kokari wajen ganin an zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta a Siriyan to saidai idan kasar Amurka ta ci gaba da nuna kiyayyar da take yiwa Gwamnatin Siriyan, hakan na iya kawo cikas wajen zartar da yarjejjeniyar.