Zarif:Amurka Ta Yiwa Yarjejjeniyar Nukiyar Iran Rikon Sakainar Kashi
(last modified Sun, 16 Jul 2017 18:49:15 GMT )
Jul 16, 2017 18:49 UTC
  • Zarif:Amurka Ta Yiwa Yarjejjeniyar Nukiyar Iran Rikon Sakainar Kashi

Ministan Harakokin Wajen Jumhoriyar Musulinci ta iran ya ce magabatan Amurka sun yi yarjejjeniyar da Iran ta Cimma da kasashen Duniya kan shirin nukiyarta na zaman lafiya rikon sakainar kashi.

A yayin da yake halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New-York na kasar Amurka, Ministan harakokin kasashen wajen na Jumhoriyar musulinci ta Iran Muhamad Jawad Zarif ya tattaunawa da tashar telbijin din CNN a wannan Lahadi inda ya ce Iran ta cika dukkanin alkawarin da ta dauka dangane da yarjejjeniyar da aka cimma na shirin nukiyar kasar na zaman lafiya kuma hukumar dake kula da makamashin Nukiya ta kasa da kasa ta tabbatar da hakan, to saidai magabatan Amurka ba su cika alkawarin da suka dauka ba.

A yayin da yake amsa tambayar cewa mai yiyuwa kasar Iran ta kera makaman kare dangi bayan yarjejjeniyar da ta cimma da manyan kasashe biyar gami da kasar Jamus, Ministan harakokin kasashen wajen na Iran ya ce a halin da ake ciki, kasar Iran na aiki da yarjejjeniyar da ta cimmawa, kuma kafin hakan ma kasar ta bayyana cewa ba ta bayan kera makaman kare dangi, kuma hukumar dake kula da makamashin Nukiya ta kasa da kasa ta tabbatar da hakan, domin haka wani zarkin da za a yiwa kasar ta Iran ba shi ta tushe.

A yayin da ya koma kan goyon bayan da kasar Iran ke baiwa kasar Siriya, Dakta Zarif ya ce Siyasar Iran a kasashen Siriya, Afganistan, Iraki da sauran kasashen yankin, a bayyane yake wato yaki da ta'addanci, duk kasar da take da gaske tana yaki da ta'addanci to jumhoriyar musulinci ta Iran za ta taimaka mata.

A yayin da ya koma kan rikicin kasar Yemen, Dakta Muhamad Zarif ya ce jumhoriyar musulinci ta Iran ta gabatar da shawarwari guda uku da za su taimaka wajen warware rikicin kasar, da suka hada da tsagaita buda wuta, taimakon kasa da kasa, tattaunawa tsakanin 'yan kasar tare da kafa Gwamnatin da Al'ummar kasar ke so, a ganin magabatan Iran wannan ita ce hanya daya cilo da za ta kawo karshen yakin kasar Yemen.

A yayin da yake mayar da martani kan labarin da Jaridar New-York Times ta wallafa na cewa kasar Iran ta mamaye kasar Iraki, Dakta Zarif ya ce Iran na goyon bayan abinda Al'ummar kasar Iraki ne suka zaba, kuma ta shiga kasar Iraki ne domin taimakonta , wanda hakan ya sha baban da wasu kasashe dake goyon bayan tsohon Shugaban kasar Saddam Hussein da kungiyoyin 'yan ta'adda.