Iran: Amurka Ce Ke Jawo Rashin Tsaro A Yankin Gabas Ta Tsakiya
Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya kara da cewa; Amurka tana kallon siyasar cin gashin kai da Iran ta ke da shi a matsayin barazana ga siyasarta ta tsoma baki a harkokin gabas ta tsakiya.
Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya kara da cewa; Amurka tana kallon siyasar cin gashin kai da Iran ta ke da shi a matsayin barazana ga siyasarta ta tsoma baki a harkokin gabas ta tsakiya.
A jiya talata ne dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ya zargi Iran da karya yarjejeniyar Nukiliya tare da bayyana Iran din a matsayin barazana mafi hatsari da Amurka ta ke fuskanta a gabas ta tsakiya.
Bahram Kasimy wanda ya ke gabatar da taron manema labaru a yau laraba ya mayarwa da Amurkan martani da cewa; Abinda Amurka ta ke yi shi shi ne kokarin kawo cikas akan duk wata moriya da Iran din za ta samu daga yarjejeniyar.
Bugu da kari, Kasimi ya yi watsi da zargin na Amurka da cewa ba shi da wani tushe.