Iran Za Ta Maida Martani Akan Yadda Amurka Ta Keta Yarjejeniyar Nukiliya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i22840-iran_za_ta_maida_martani_akan_yadda_amurka_ta_keta_yarjejeniyar_nukiliya
Shugaban cibiyar da ke bibiyar aiki da yarjjeniyar Sayyid Abbas Irakche ne ya bayyana haka a hira da tasha ta 1 da jamhuriyar musulunci ta Iran.
(last modified 2018-08-22T07:00:29+00:00 )
Aug 03, 2017 02:17 UTC
  • Iran Za Ta Maida Martani Akan Yadda Amurka Ta Keta Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban cibiyar da ke bibiyar aiki da yarjjeniyar Sayyid Abbas Irakche ne ya bayyana haka a hira da tasha ta 1 da jamhuriyar musulunci ta Iran.

Irak chi, ya kuma kara da cewa; Yarjejeniyar tana a matsayin wani babban cikas ne a gaban Amurka na kakaba ma ta takunkumi mai tsanani da su ka hada da na man fetur.

Abbas Arak chi ya kuma bayyana cewa; Abinda ya ke razana Amurka shi ne yadda  Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ke kara samun karfi da bunkasa.

Har ila yau Irak chi ya ce; Abinda Amurka ta ke son gani shi ne ta ingiza Iran ta fice daga cikin yarjejeniyar ta Nukiliya, sai dai wajibi ne ga Amurka ta san cewa hakan ba za ta faru ba.

A ranar 18 ga watan Yuli da ya shude ne dai majalisar shawarar musulunci ta Iran ta amince da a maida martani ga ta'addancin Amurka.

A makon da ya gabata ne dai Majalisar dokokin Amurka ta amince da kakabawa Iran sabbin takunkumai. Kuma a jiya laraba ne shugaban kasar Donald Trump ya rattaba hannu akai.