Dubban Alhazan Iran Sun Isa Saudiyya Domin Aikin Hajjin Bana
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i22852-dubban_alhazan_iran_sun_isa_saudiyya_domin_aikin_hajjin_bana
Dubban alhazan kasar Iran sun isa kasar saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
(last modified 2018-08-22T07:00:29+00:00 )
Aug 03, 2017 12:57 UTC
  • Dubban Alhazan Iran Sun Isa Saudiyya Domin Aikin Hajjin Bana

Dubban alhazan kasar Iran sun isa kasar saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto daga shugaban hukumar alhazai ta kasar Iran Sa'id Auhadi a yau yana cewa, ya zuwa yanzu dubban alhazan kasar Iran ne suka isa birnin Madina mai alfarma inda suke gudanar da ziyara a wurare masu tsarki kafin su wuce birnin Makka mai alfarma.

Auhadi ya ce nan da 'yan kwanaki masu zuwa za a kammala kwashe alhazan kasar ta Iran kimanin 86,500 zuwa Saudiyyah domin gudanar da aikin hajjin bana, bayan sun samu dukkanin horon da ya dace kan yadda ake gudanar da aikin hajji.

Bisa tsarin hukumar alhazan kasar Iran dai a kan bayar da horo ga maniyyata, musamman wadanda ba su taba zuwa aikin hajji ba, ta yadda har a kan yi samfurin dakin Ka'abah da ma wasu wuraren masu tsarki, domin nuna musu yadda ake gudanar da aikin hajji a aikace.

A shekarar da ta gabata masu rike da madafun iko a kasar Saudiyya sun hana dubban alhazai daga kasashen Iran, Yemen da kuam Syria sauke farali, saboda dalilai na siyasa, inda a shekarar bana ma, mahukuntan na masarautar Al Saud sun haramtawa dubban alhazai sauke farali daga kasashen Yeman da kuma Syria, kuma akwai yiwuwar hakan ya shafi maniyyata daga kasar Qatar.