Jamio'in Iran Fiye Da 30 Suna Cikin Mafi Tasiri A Duniya
Cibiyar da take tantance ingancin jami'oi a duniya ( ISC) ta shigar da jami'oin Iran 31 a cikin jerin mafi tasiri a duniya a fagen fasaha da kere-kere.
Daga cikin jami'oin Iran da rahoton cibiyar ta ( ISC) na bayan nan ya ambata da akwai jami'oin Tehran, shirz, Tarbiyatu Mudarras, Shiraz, Firdausi Mashhad, Tabriz, Shahid Beheshti, Saminan, da Shahid Bahonar.
Sai kuma jami'oin Karman, Isfahan, Gilan, Arumiyyah, Razy, Kashan, Bu Ali-Sina, Yazd, sai kuma jami'ar kasa da kasa ta Imam Khumain.
Sauran jami'oin da su ka shiga cikin rahoton na cibiyar ( ISC) sune Kahlij Fars Bushehr, Muhakkin Ardabili, Shahri Kurd, da Yasuj.
Kaso 1% ne na jami'oin duniya suke shiga cikin mafi tasiri a duyniya, kuma duk bayan watanni biyu ana sabunta su.