Sharhi: Amincewar Majalisar Iran Ga Kudurin Mayar Da Martani Da Barazanar Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23190-sharhi_amincewar_majalisar_iran_ga_kudurin_mayar_da_martani_da_barazanar_amurka
'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran sun amince da kudurin na mayar da martani ga sabbin takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar Iran da kuma kokarin mulkin mallaka da take son yi wa kasashen yankin Gabas ta tsakiya inda suka wajabta wa gwamnatin kasar ci gaba da karfafa shirin kare kai da mayar da martani cikin gaggawa da dakarun Iran din suke da shi.
(last modified 2018-08-22T07:00:32+00:00 )
Aug 15, 2017 01:23 UTC
  • Sharhi: Amincewar Majalisar Iran Ga Kudurin Mayar Da Martani Da Barazanar Amurka

'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran sun amince da kudurin na mayar da martani ga sabbin takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar Iran da kuma kokarin mulkin mallaka da take son yi wa kasashen yankin Gabas ta tsakiya inda suka wajabta wa gwamnatin kasar ci gaba da karfafa shirin kare kai da mayar da martani cikin gaggawa da dakarun Iran din suke da shi.

'Yan majalisar sun cimma wannan matsayar ne a zaman da suka yi a shekaran jiya Lahadi (13-08-2017) inda 'yan majalisar 240, suka kada kuri'ar amincewa da kudurin da suka kira shi da kudurin mayar da martani ga "ta'addancin Amurka da kokarin mulkin mallakanta" a yankin Gabas ta tsakiya.

Kudurin dai ya bukaci gwamnatin kasar Iran da dakarun sojin kasar da su tsara da kuma fitar da wata siyasa da tinkarar siyasar take hakkokin bil'adama da Amurka take gudanarwa a duniya bugu da kari kan ware Dala miliyan 260 don karfafa shirin makamai masu linzami na Iran da kuma wasu dala miliyan 260 ga dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar don  fada da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kasashen duniya dai suna tsara siyasar tsaron kasashensu ne bisa yanayin da suke ciki kana kuma gwargwadon irin barazanar da suke fuskanta. A saboda haka kasar Iran, bisa la'akari da yankin da take, tana fuskantar wasu nau'oi na barazana wadanda hakan ya tilasta mata tsara wasu tsare-tsare don fada da kuma fuskantar wadannan barazanar. To sai dai kamar yadda jami'an kasar suka sha fadi, dukkanin wadannan tsare-tsare na kariya da take da su, ba za su taba zama wata barazana ga sauran kasashe ba; face dai wani shiri ne na fada da barazanar da take fuskanta. Daga cikin siyasar kare kai da Iran ta dauka har da karfafa shirin makamanta masu linzami. A saboda haka ne Amurka a koda yaushe take ta kokari wajen raunana kasar Iran, don cimma wasu manyan manufofi guda biyu: wato: (1). Kawo karshen karfin makamai masu linzami na Iran ta hanyar kirkirar tuhuma maras tushe na cewa wadannan makaman suna iya zama barazana ga duniya, sai kuma na (2). Ragewa ko kuma kawo karshen irin tasirin da Iran take da shi cikin sansanin 'yan gwagwarmaya ta hanyar tuhumarta da goyon bayan ayyukan ta'addanci, dukkanin wadannan dai da nufin  ganin bayan tsarin Jamhuriyar Musulunci da ke iko a kasar.

Bisa la'akari da kyakkyawar fahimtar wannan makirci na Amurka ne ya sanya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya tsaya kyam wajen ganin Iran ta tsaya da kafafunta a fagen karfin kare kanta. A saboda haka ne ma a wani jawabi da ya yi a yayin rangadin da ya kai masana'antar kera makamai na Iran yake bayyana cewar: "A daidai lokacin da ma'abota girman kan duniya suka baza dukkanin komarsu ta zalunci ba tare da komai kashin tausayi ba, haka nan kuma a gaban idanuwan duniya suke kai hare-hare kan asibitoci da wajajen daurin aure inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu da sunan fada da ta'addanci, sannan kuma babu wata cibiya da kasa da kasa da ta ce musu uffan, to a irin wannan yanayin wajibi ne a kara karfafa irin karfin kariya da ake da shi don masu tinkaho da karfin su ji cewa ba fa za su iya sha ba".

A saboda haka Iran, a fagen kariya da kai hatta ma da mayar da martani ga duk wata barazana, ta kai wani matsayi na kolin gaske da babu wani da ke musun hakan. Ko shakka babu hari da makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran din suka kai garin Deir Zur na kasar Siriya da tarwatsa sansanonin 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh a matsayin mayar da martani da harin da suka kawo birnin Tehran a ranar 7 ga watan Yuni, babban dalili ne da ke tabbatar da irin karfin da Iran take da shi na kare kanta da kuma tinkarar makiya. Don haka ko shakka babu wannan kuduri da 'yan majalisar na Iran suka sanya wa hannu wani lamari ne da ke nuni da matsayar da Iran take da shi na kare kanta daga duk wata barazana ta makiya.