Yakamata Amurka Ta Ji Kunyar Magana Kan Take Hakkin Bil'adama - Ayat. Khatami
Limamin da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta ji kunyar bayyana ra'ayinta dangane da take hakkin bil'adama a sauran kasashen duniya.
Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa harin da wani matashi mai akidar wariyar launin fata ya kaiwa masu zanga-zangar yin Allah wadai da wariya a jiyar Vejinia ta kasar Amurka a ranar Asabar da ta gabata, da motan da yake tukawa, wanda kuma ya jawo mutuwar wata mata da raunata wasu mutane 19 ya nuna cewa yakamata gwamnatin Amurka ta magance matsalolinta na wariya kafin ta ce zata yi magana na wasu kasashen duniya.
Limamin har'ila yau a cikin khudubarsa ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci wadanda aka kai a kasar Afghanistan da kuma Basalona na kasar Espania. Ya kara jaddada bukatar yaki da yan ta'adda a ko ina suke, sannan ya kiraye mutanen Amurka da kasashen turai da su bukaci gwamnatocinsu su daina tallafawa ayyukan ta'addanci.
Dangane da shaheed Muhsn Hujaji wanda yan ta'adda suka yanka a kasar Siria, Ayatullah Khatami ce matasan Iran suna nan kamar tokororinsu a farkon juyin juya hali, ya kuma yaba da sanarwan dakarun kare juyin juya halin musulunci ta bayar na cewa zata dauki fansar shahadarsa. .
Daga karshe limamin ya yi tsogaci kan sabuwar gwamnati ta Dr hassan Ruhani, inda ya bukaceta da ta kasance mai khidimawa addini da mutanen kasar iran, da kuma duk wani ci gaban kasar.