Kuri'ar Amincewa Da Ministocin Sabuwar Gwamnatin Shugaba Hasan Ruhani
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23386-kuri'ar_amincewa_da_ministocin_sabuwar_gwamnatin_shugaba_hasan_ruhani
A jiya Lahadi ne dai majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ta kawo karshen zaman tantance ministoci 17 da shugaba Hasan Ruhani ya gabatar mata don amincewa, inda majalisar ta amince da ministoci 16 kana guda kuma ya gagara samun amincewar majalisar.
(last modified 2018-08-22T07:00:34+00:00 )
Aug 21, 2017 00:44 UTC
  • Kuri'ar Amincewa Da Ministocin Sabuwar Gwamnatin Shugaba Hasan Ruhani

A jiya Lahadi ne dai majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ta kawo karshen zaman tantance ministoci 17 da shugaba Hasan Ruhani ya gabatar mata don amincewa, inda majalisar ta amince da ministoci 16 kana guda kuma ya gagara samun amincewar majalisar.

Rahotanni sun bayyana cewar Habibullah Bitaraf, wanda shugaba Ruhani ya gabatar da sunansa a matsayin wanda yake so ya zama Ministan Makamashi na kasar Iran din shi ne ya gagara samun kuri'un da ake bukata wajen rike wannan mukamin, inda 'yan majalisa 133 suka kada kuri'ar amincewa da shi, 132 kuma suka ki amincewa kana wasu 17 kuma suka ki kada kuri'ar.

Kuri'ar amincewar da majalisar ta kada wa sabuwar gwamnatin ta shugaba Ruhani yana a matsayin share fagen kafa sabuwar majalisar ministocin gwamnatin ta Iran duk da cewa rabin ministocin daman sun kasance a gwamnatin Ruhanin da ta shude. Da dama dai suna ganin irin kuri'un amincewar da 'yan majalisar suka kada wa sabuwar gwamnatin a matsayin wata alama ta bude sabon shafin aiki tare tsakanin gwamnati da majalisar. A don haka dukkanin idanuwa za su koma kan shugaban kasar da sabuwar gwamnatin tasa wajen ganin matakan da gwamnatin za ta dauka wajen biyan bukatun al'ummar kasar tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Ko shakka babu babbar matsalar da gwamnatin za ta fuskanta ita ce matsalar tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma. Duk da cewa sabuwar gwamnatin ta bangarori daban-daban ta yi kama da gwamnatin da ta shude din wanda hakan yana nuni da ci gaban ayyuka da tsare-tsaren da wancan gwamnatin take kai duk kuwa da cewa akwai yiyuwar a samu 'yan wasu sauye-sauye nan da can. A saboda haka ne da dama suke ganin akwai gagarumin aiki a gaban sabuwar gwamnatin wajen isa ga fatan da mutane suke da shi a kanta da kuma kai wa ga manufofin tsarin tattalin arziki na dogaro da kai da Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sanar da kuma fatan ganin an cimma wanda hakan ne zai iya kai kasar ga tudun na tsira daga irin kiyayya da makirce-makircen da makiya suke kulla wa kasar ba dare ba rana.

Masana dai suna ganin wajibi ne gwamnatin ta ba da muhimmanci ga batutuwa irin su karfafa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, karfafa alaka ta kasa da kasa da kuma karfafa bangarori daban-daban na tattalin arzikin arziki musamman batun fada da ta'annuti ga tattalin arziki da kuma fasa kwabrin kayayyaki zuwa cikin gida.

Kamar yadda kuma ko shakka babu kiyaye tsaron kasa da kuma fada da duk wata barazana ta ciki da waje lamurra ne da za su taimaka wa wannan shiri da ake da shi da kuma kai shi zuwa ga manufar da aka sanya a gaba; wanda babbar alamar da ke nuni da muhimmancin wannan bangare na tsawo shi ne irin kuri'u masu yawan gaske da ministocin tsaron kasa da kuma tabbatar da tsaron cikin gida suka samu daga wajen 'yan majalisar a kuri'ar da suka kada don amincewa da ministocin da aka gudanar a jiya Lahadin.