Iran:Ranar Tunawar Da Shahadar Ali Raja'i Da Bahonar
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23668-iran_ranar_tunawar_da_shahadar_ali_raja'i_da_bahonar
Ranar 30 ga watan Augusta, wacce ta yi daidai da 8 ga watan Shahribar ce, ranar kasa ta fada da ta'addanci a Iran.
(last modified 2018-08-22T07:00:37+00:00 )
Aug 30, 2017 02:24 UTC
  • Iran:Ranar Tunawar Da Shahadar  Ali Raja'i Da Bahonar

Ranar 30 ga watan Augusta, wacce ta yi daidai da 8 ga watan Shahribar ce, ranar kasa ta fada da ta'addanci a Iran.

Kungiyar ta'addanci ta MKO mai fada da tsarin musulunci a Iran ce dai ta kai harin da ya yi sanadiyyar shahadar  shugaban kasa Muhammad Ali Raja'i da kuma Pira minista Muhammad Jawad Bahonar.

Shahidan biyu dai sun yi fice a lokacin mulkinsu da maida hankali wajen warware matsalolin al'umma, sannan kuma da rayuwa mai suki da kaskantar da kai da suka yi.

A halin da ake ciki a yanzu a duniya ta'addanci ne babbar matsalar da ake fuskanta, wanda ya jefa rayuwar al'ummu cikin hatsari.