Iran Ta Bayyana Cewa: Tsaurin Ra'ayi Yana Daga Cikin Manyan Matsalolin Duniya
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tsaurin ra'ayi da akidar wuce gona da iri kan al'umma, matsaloli ne da suka game duniya baki daya.
A ganawarsa da ministan harkokin wajen Fadar Vatican ta darikar katolika ta mabiya addinin Kirista Paul Richard Gallagher a yau Laraba a birnin Tehran: Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya jaddada wajabcin gudanar da zaman tattaunawa a tsakanin mabiya addinai da mazhabobi daban daban da nufin samun mafita kan matsalolin da suke kunno kai da sunan addini musamman tsaurin ra'ayi da akidar wuce gona da iri kan juna.
Har ila yau Jawad Zarif ya jaddada bukatar taimakon dukkanin kasashe domin kawo karshen kashe-kashen gillar da ake yi wa al'ummar musulmin kasar Myanmar tare da kokarin korarsu daga kasarsu ta gado.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen Fadar Vatican Paul Richard Gallagher yayi nuni kan yadda kasar Iran da fadar Vatican suke aiki tare kafada da kafada da nufin kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya musamman shawo kan matsalar 'yan gudun hijira da tsaurin ra'ayin addini. Kamar yadda Paul Richard ya tabo batun kasar Myanmar da irin kokarin da fadar Vatican ke yi da nufin kawo karshen rikicin kasar.