Shuwagabannin Kasashen Musulmi Zasu Tattauna Batun Kisan Kiyashi A Kan Musulman Myanmar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammaf Jawad Zareef ya bayyana cewa shuwagabvannin kasashen Musulmi Zasu tattauna batun kisan kiyashin da ake wa musulmin kasar Myanmar a taron kan ci gaban ilmi da fasahan da suke gudanarwa a halin yanzu a kasar Qazakistan.
Muryar JMI ta nakalti Zareef yana fadar haka a jiya Asabar a kasar Qazakistan inda yake cikin tawagar da shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya je da su taron na Qazakistan.
Ministan ya kara da cewa kafin taron na Qazakistan dai ya tattauna da tokororinsa na kasashen musulmi da dama kan kisan kiyashin da ake wa musulman kasar ta Myanmar, kuma kasar Qazakistan a matsayin mai masaukin baki a wannan taron da kuma kasar Turkiya a matsayin mai shugabancin Taron sun yi alkawari za'a tattauna wannan batun don daukar matakin da ya dace kan wannan matsalar.