Tawagar Wakilan Gwamnatin Iran Ta Ziyarci Sansanin 'Yan Gudun Hijira Musulmin Myanmar
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i24097-tawagar_wakilan_gwamnatin_iran_ta_ziyarci_sansanin_'yan_gudun_hijira_musulmin_myanmar
Tawagar wakilan gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar musulmin kasar Myanmar ko kuma Burma da ke yankunan da suke kan iyaka tsakanin kasar Bangaledesh da Myanmar.
(last modified 2018-08-22T07:00:42+00:00 )
Sep 17, 2017 02:02 UTC
  • Tawagar Wakilan Gwamnatin Iran Ta Ziyarci Sansanin 'Yan Gudun Hijira Musulmin Myanmar

Tawagar wakilan gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar musulmin kasar Myanmar ko kuma Burma da ke yankunan da suke kan iyaka tsakanin kasar Bangaledesh da Myanmar.

Tawagar wakilan gwamnatin Iran karkashin jagorancin Ibrahim Rahimipoor mataimakin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasashen Asiya a jiya Asabar ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijirar musulmin kasar Myanmar ko kuma Burma da ke yankunan da suke tsakanin kasashen Bangaledesh da Myanmar, inda jami'an kasar Iran suka saurari bukatun 'yan gudun hijira tare da jin irin halin kuncin da suka shiga a fagen rayuwa.

Har ila yau tawagar wakilan gwamnatin kasar ta Iran ta gabatar da kayayyakin jin kai ga al'ummar musulmin Myanmar ko kuma Burma da nufin rage musu rayuwar kunci da suke ciki a fagen rayuwa.

Tun a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata ne sojojin gwamnatin Myanmar ko kuma Burma da taimakon mabiya addinin Bouza na kasar suka fara kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya da suke lardin Rakhine a yammacin kasar, inda zuwa yanzu suka kashe dubban mutane tare da jikkata dubban daruruwa baya ga tilastawa wasu fiye da 400,000 yin gudun hijira daga muhallinsu.